
Shugaban bankin Access Bank, Roosevelt Ogbonna ya sayi gidan dala Miliyan $20 a Landan.
!Ya sayi gidanne a unguwar masu kudi da ake cewa, Billionaires’ Row kamar yanda kafar Bloomberg ta ruwaito.
Rahotan yace da farko kudin gidan sun fi haka amma daga baya aka masa sauki ya kuma saya.
Wannan gida da ya siya yana daga cikin ciniki masu tsada da aka yi a Landan wanda ya dauki hankula.