
Sabon zababben shugaban karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina, Hon. Aminu Dan Hamidu, ya rasu kasa da wata biyu bayan karbar rantsuwar kama aiki.
Hon. Hamidu, wanda ya hau kujerar shugabancin karamar hukumar a watan Afrilu 2025, ya rasu a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025. Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwarsa a hukumance ba. Sai dai rahotanni da ba a tabbatar da su ba na nuna cewa yana fama da rashin lafiya tun kafin rasuwarsa.
Kaula Mohammed, sakataren yada labarai ga Gwamna Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa.
A cikin sanarwar, Gwamna Radda ya bayyana alhini da jimamin da ya shiga sakamakon rasuwar Hon. Hamidu, yana bayyana mamacin a matsayin “dan jam’iyya na kwarai, tsohon ma’aikacin gwamnati mai kwarewa, kuma ɗan siyasa na ƙasa da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya