
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara kasar Amurka dan jawo hankalin kasar da fahimtar da ita halin da ake ciki a Najeriya ba kamar yanda ake cewa ana yiwa Kiristoci Khisan Khiyashi ba.
Rahoton yace Shugaban kasar Amurkar ya wakilta mataimakinsa, JD Vance ya gana da shugaba Tinubu a yayin ziyarar.
Kafar Sahara Reporters ce ta bayyana haka inda tace ta samu bayanan ne daga fadar shugaban kasa Bola Tinubu.
Hakan na zuwane a yayin da ake tsaka da fargabar kawo hari na kasar Amurka a Najeriya.