
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara yakin neman zaben shekarar 2028.
A shekarar 2028 ne kasar Amurka zata saken yin zaben shugaban kasa.
Sannan kudin tsarin mulkin kasar ya haramta a zabi shugaban kasa sau uku amma duk da haka Trump yace ya gano wata hanyar da zai yi nasara.

Dan shugaban kasar, Eric Trump ne da kansa ya fara tallar baban nasa inda ya saka hular dake tallata babban nasa a zaben shekarar 2028.
Wata majiya dai tace Trump na kokarin saka mataimakinsa, JD Vance ne ya fito takarar shugaban kasa inda shi kuma Trump din zai masa mataimakin shugaban kasa.
Bayan an ci zabe, Trump zai bukaci JD Vance ya sauka inda shi kuma sai ya zama shugaban kasar.