
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, maimakon ya rika aika jirage suna mayar da mutane kasashensu, zai fara baiwa ‘yan Cirani dala dubu 1 dan su rika biyan kudin jirgi suna komawa kasashensu.
Ma’aikatar tsaro ta Department of Homeland Security ce ta bayyana hakan a sanarwar da ta fitar inda tace duk dan cirani da bashi da takardun zama a kasar da ya yadda zai koma kasarsa, za’a bashi dala $1000.
Hukumar tace wannan ce hanya mafi sauki wadda kuma ba sai an kama mutum an wulakantashi ba kamin ya bar kasar.
Tace kamawa da tsarewa da mayar da mutane kasarsu yanasa kasar ta Amurka kashe Dala $17,000 akan kowane mutum.
Dan haka baiwa mutane dala $1000 ya fi sauki idan sun yadda su koma kasarsu.