Friday, December 5
Shadow

Shugaban Sojojin Najeriya ya bayyana masu daukar nauyin matsalar tsaro da abinda suke son cimmawa a Najeriya

Shugaban hedikwatar tsaro ta kasa, Christopher Musa ya zargi cewa, yawaitar matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya na da alaka da gabatowar zaben 2027.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Yace idan ba haka ba, ta yaya, shekarar data gabata an samu rahoton raguwar matsalar tsaro sosai amma a wannan shekarar abubuwa su kara dagulewa?

Yace ‘yan siyasa ne ke daukar nauyin ‘yan Bindigar inda ya kara dacewa abinda suke son cimma shine bata sunan Gwamnati ace bata kokari.

Yace amma abin takaici shine ta yaya zaka rika kashe mutanen da kake son mulka?

Karanta Wannan  Sojan Najeriya da ya hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga waja dake gini dan ya rusashi nata shan yabo wajan 'yan Najeriya

Ya kuma zargi cewa, bayan masu daukar nauyin ‘yan Bindigar a cikin gida, akwai kuma masu daukar nauyin ‘yan Bindigar daga kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *