Tuesday, April 7
Shadow

Shuwagabannin tsaron Najeriya na shan suka bayan kìsàn mutane 250 a cikin makonni 2, ana zargin sun gaza

Masu sharhi akan al’amuran tsaro na sukar shuwagabannin hukumomin tsaro na Najeriya saboda yawaitar kashe-kashen da ake yi musamman a jihohin Arewa.

Ana ganin matsalar tsaron ta sha kan su ko kuma basa daukar matakan da ya kamata dan magance matsalar.

Hakan na zuwanw yayin daka yi kashe-kashe a jihohin Filato, Borno, Katsina, da Benue.

Hakanan ga kuma wata sabuwar kungiyar masu ikirarin jihadi me suna Mamuda data bayyana a jihar Kwara dake arewa maso tsakiyar Najeriya.

Manyan shuwagabannin hukumomin tsaro a Najeriya sune Gen. Christopher Musa; Chief of Army Staff, Lt-Gen. Olufemi Oluyede; Chief of Air Staff, Air Marshal Hassan Abubakar, Chief of Naval Staff, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Karanta Wannan  Barayi sun sace mashina 3 yayin da ake sallar Taraweeh a Abuja

Sannan akwai babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Ministan Tsaro, Muhammad Badaru da karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

An kashe mutane 250 a cikin sati biyu da suka gabata a jihohin Plateau, Benue, Borno, Kebbi, Katsina, Abia, da Kwara.

Jihar Plato ce ta fi fuskantar matsalar inda aka kashe mutane 113.

A jihar Benue kuma mutane 55 ne aka kashe.

Sai kuma a jihar Kwara aka kashe mutane 15.

Lamarin tsaron yasa mutane na kira ga hukumomi da su dauki mataka kawo karshen matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *