
Rahotanni da hutudole ke samu daga garin Gubio na jihar Borno na cewa, Kungiyar ÌSWÀP ta yi yunkurin kaiwa garin hari ranar Litinin amma Sojoji suka dakile harin.
Saidai Ranar Talata, Kungiyar ta sake durfafar garin inda ta nufi sansanin sojojin da afka mai da yaki.
Saidai mutanen garin na sanar da sojojin, a wannan karin sai aojojin suka tsere.
Rahoton yace ko da kungiyar ta ji sojojin sun tsere sai ta fasa kai harin suka juya.
An ce dai daga baya sojojin sun koma sansanin nasu.