ADC: “Ni ba zan haɗa kai da ɓarayi don yaƙar ɓarayi ba ” — Sowore ya caccaki haɗakar jam’iyyun adawa.

Dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa ba zai taba shiga cikin hadakar ’yan adawan da ke neman kifar da jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027 ba.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Sowore ya ce ba zai iya hada kai da wasu fitattun ’yan siyasa da ya zarga da rusa Najeriya ta hanyar cin hanci da rashawa, cin amanar kasa da zalunci ba.
“Ban taba hada kai da Bola Ahmed Tinubu wajen rarraba hodar iblis a birnin Chicago ba,” in ji Sowore.
“Ban hada kai da Atiku Abubakar wajen wawure dukiyar Hukumar Kwastam ba. Ban taba shiga cikin barnar David Mark wanda ya saci kudaden da aka ware don gyara wayoyinmu sannan ya taimaka wajen murkushe burin dimokuradiyyarmu a ranar 12 ga Yuni ba.”
A cikin wannan suka mai zafi ga tsarin siyasar Najeriya, Sowore ya jero wasu daga cikin manyan ’yan siyasa da ya ce sun taka rawa wajen lalata kasar, ciki har da tsofaffin gwamnoni, ministoci da ‘yan takarar shugaban kasa.
Sowore ya ki amincewa da kira da ake yi masa da ya sassauta tsayuwarsa kan akida saboda bukatar siyasa, yana mai cewa:
“Ban taba shiga cikin kungiyoyin ’yan fashi da makami ba. Ban taba rantsuwa da wata kungiya ko tsari na sirri — ko da kuwa suna da farin jini, iko ko ban sha’awa — ba.”