‘
Yan sanda a jihar Osun sun kama wani limamin masallaci me suna Babasanya-Araka da zargin yin lalata da karamar yarinya.

Lamarin ya farune a garin Ede na jihar, kuma ya tayar da hankulan jama’ar garin.
Mutane sun taru suka fara dukan limamin saidai jami’an tsaro sun je sun kwaceshi.
Kakakin ‘yansandan jihar, Abiodun Ojelabi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace da suka je Wajan har Amotekun sun kama limamin inda suka damka musu shi.
Yace zasu gudanar da bincike akanshi kamin su mika shi zuwa SCID.
Wani shaida yace yarinyar da ake zargin limamin da yin lalata da ita shekarunta 8 kuma ta bace ana nemanta sai gata an ganta tana kuka jini na zuba a gabanta.
Yace Tuni ka kaita Asibiti.