Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta kama a zanga-zangar tsadar rayuwar da aka yi sun magantu kan abinda ya faru.
A hirar da jaridar Punch ta yi dasu, daya daga cikin wadanda suka fito daga Kano, Umar Ali me shekaru 15 ya bayyana abinda ya faru.
Yace ba’a basu abinci yanda ya kamata wani lokacin sai da suka yi kwanaki 3 sannan aka basu abinci kuma abincin ba mai yawa ba gashi babu dadi.
Umar Ali yace shi bai yi zanga-zangar ba ya fita ne zuwa wajan da yake aiki a Kwana Hudu dake Ungoggo inda a nan ne aka kamashi.
Yace an ajiyesu a daki me duhu basa ganin rana, shiyasa bayan da aka fito dasu ko gani basa yi da kyau.
Shima wani matashi me suna Ibrahim Aliyu Musa ya bayyana cewa an ajiyesu a guri daya da muggan masu laifi.
Shima yace suna kwanaki da yawa babu abinci inda yace abincin ba dadi, ana basu wake da safe sai Shinkafa da rana sai Gabza da dare.
Shima wani dan shekaru 13 da aka kama a Gadon Kaya bisa zargin daga tutar kasar Rasha ya bayyana cewa bai aikata hakan ba.
Saidai kakakin ‘yansandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya musanta ikirarin yaran inda yace basu hadasu da muggan masu laifi ba, kawai ana son batawa hukumar ‘yansandan Najeriya sunane.