
Rahotanni sun bayyana cewa, sunan Muhammad ya shiga cikin jerin sunaye mafiya shahara a kasar Ingila inda aka sakawa jarirai 4,661 sunan.
A Brussels kuwa sunan Mohamed shine yazo na daya.
Hakanan a Jamus ma sunan Muhammad ya shahara sosai.
A Netherlands kuwa sunan Muhammad shine ya zo na 2.
A Norway kuwa sunan Mohammed na daya yazo.
A Ireland ma sunan Muhammad ya taba zuwa na daya a shekarar 2022.