Friday, December 5
Shadow

Talakawa na karuwa sosai a Najeriya, mutane da yawa basa samun Naira dubu biyar a rana>>Inji Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talakawa na karuwa sosai a Najeriya dama wasu sauran kasashe 38 na Duniya.

Bankin yace hakane a wani babban rahoto da ya fitar tun bayan bullar cutar Korona a shekarar 2020.

Bankin yace jimullar mutane Miliyan 421 ne ke fama da matsanancin talauci a Duniya.

Bankin ya kara da cewa, mutanen basa samun akalla Dala $3 a kullun wanda kwatankwacin Naira dubu biyar kenan.

Bankin ya alakanta hakan da matsalolin tsaro da sauransu.

Ya kuma yi gargadin yawan matalautan na iya karuwa zuwa mutane Miliyan 435 nan da shekarar 2030.

Karanta Wannan  David Mark zai shagabanci jam'iyyar ADC ta hadakar 'yan adawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *