Wednesday, May 21
Shadow

Tashin bàm ya kàshè mutum 26 a jihar Borno

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa aƙalla mutum 26 ne suka rasu ranar Litinin sakamakon tashin wani bam da motar da suke ciki ta taka a kan hanyar da ke tsakanin garin Rann zuwa Gmaboru Ngala.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun haɗa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.

Bam ɗin da ake zaton ƙungiyar Bòkò Haram ce ta dasa binne shi, ya kuma jikkata aƙalla mutum da dama waɗanda suke asibiti domin samun kulawa.

Duk da cewa al’ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Bòkò Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Buhari Ya Gwangwaje Mawaƙi Ɗan Soja Da Kyautar Kuɗi Dala Dari A Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *