
Yara 5 ne suka jikkata bayan tashin wani bam a karamar hukumar Mafa dake jihar Borno inda hannun daya daga cikin yaran ya tsinke.
Lamarin ya farune ranar alhamis da misalin karfe 2:25 na rana inda yaran suka je suna wasa da Bam din ba tare da sun sani ba.
Bam din dai an boyeshi ne a cikin bulo a kusa da inda ake gina Masallacin Juma’a na Mafa.
Yaran su 4 ne sai yarinya 1 Abdullahi Umar, Musa Mele, Fatima Abatcha, Abba Kawu Muhammed, da Khalid Alhaji Bukar.
Daya daga cikin yaran ya rasa hannun shi inda kuma aka garzsya da guda 4 zuwa Asibitin Maiduguri amma guda daya da hai ji ciwo sosai ba an kaishi Asibitin Mafa inda aka bashi magani aka sallameshi.
Tuni ‘yansanda da suka kware wajan kwance Bam suna kai dauki wajan.