
Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya wasa bayan shekaru 15 da ya shafe yana buga wasa.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta.
Ahmed Musa ya bugawa Najeriya wasanni 111 inda kuma shine wanda yafi kowane dan wasa yawan kwallaye a gasar cin kofin Duniya a Najeriya.