Friday, December 5
Shadow

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata.

Tawagar gwamnatin tarayya ta isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da jana’izar fitaccen ɗan kasuwa, dattijo, Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Madina, wanda ya rasu a ƙasar Dubai yana da kimanin shekaru 94 a Duniya, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma ministan tsaron ƙasa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ta haɗa da ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN, da ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Muhammad Idris, da ƙaramin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata.

Sauran ƴan tawagar sun haɗa da: manyan malaman addinin musulunci, Dakta Bashir Aliyu Umar, Shaik Aminu Ibrahim Daurawa da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad, babban limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Kalli Hotunan yanda Motar rusau ta bayyana a gidan Sarkin Nasarawa, inda Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune yanzu haka

Tawagar za ta haɗu da membobin hulɗar diplomasiyya na Najeriya da ke birnin Madina, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya, waɗanda suka gudanar da shirye-shiryen jana’izar a yau Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *