Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu kan salon mulkin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi a Najeriya.
Kungiyar tace salon mulkin na Tinubu da tsare-tsare na mugunta sun sa mutane miliyan 14 sun tsunduma a cikin talauci a gwamnatinsa.
Kungiyar tace a shekarar 1999 ta goyi bayan Bola Ahmad Tinubu ya zama gwamnan Legas kuma ta ga irin salon mulkinsa dan hakane yasa tace babu dalilin da zai sa da ya fito takarar shugaban kasa ta goyi bayansa.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar ta Afenifere Ayo Adebanjo, ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Justice Faleye.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Tinubu da ya gyara nuna fifiko da yakewa Yarbawa wajan bayar da mukaman gwamnati a mulkinsa.