Tuesday, January 7
Shadow

Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da rashawa a 2024 – OCCRP

Shugaban Najeriya Bola Tinubu na cikin na gaba-gaba a jerinn mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da kuma aikata cin hanci da rashawa, a cewar rahoton cibiyar kula da aikata manyan laifuka da rashawa ta duniya.

CIbiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP) kan nemi ‘yanjarida da ƙwararru da ɗaiɗaikun mutane su kaɗa ƙuri’a wajen zaɓen mutanen da suka fi aikata tsararrun laifkuka a ɓangaren cin hanci da rashawa duk shekara.

Tinubu ne ya zo na uku a jerin, yayin da tsohon Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zo na ɗaya “saboda abubuwan da suka faru a ƙasar a baya-bayan nan,” in ji OCCRP.

Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ko Tinubu kansa ba su ce komai ba game da sakamakon ƙuri’ar.

Karanta Wannan  Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya nada diyarsa a matsayin First Lady bayan da matarsa ta rasu

Duk da cewa shi ne ya fi kowa yawan ƙuri’u, Shugaban Kenya William Ruto ne ya zo na biyu bayan ya samu ƙuri’a sama da 40,000.

Sama da shekara 10 kenan ana fitar da sakamakon ƙuri’ar, inda a wannan karon aka bai wa Shugaban Ƙasar Equatorial Guinea “lambar zambo ta wanda bai taɓuka komai ba” (lifetime non-achievement award) a matsayin shugaban da ya fi kowa daɗewa a kan mulki a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *