
Kungiyar kare muradun yarbawa ta YCG ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba na gari wanda rahama ne ga ‘yan Najeriya.
Kungiyar tace tsare-tsaren shugaba Tinubu sun taimaka wajan samar da tsaro, ga rayuwa da dukiyoyin jama’a.
Kungiyar tace a cikin shekaru 2 da shugaba Tinubu yayi yana mulki, Gwamnatinsa ta samar da tsaro da kara karfin tattalin arzikin Najeriya.
Wakilan Kungiyar Olugbemga Oyewusi, Mrs Buky Tunde Oshunrinde, ne suka bayyana hakan a sanarwar da suka fitar ga manema labarai.
Sun ce Yabo Shugaba Tinubu ya cancanta ba barazana da zagi ba.