Friday, December 5
Shadow

Tinubu siyasa ya iya, bai iya Mulki ba>>Inji Dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo ya bayyana cewa, shuaban kasa, Bola Ahmad Tinubu siyasa ya iya amma bai iya mulki ba.

Ya bayyana hakane a hirar da kafar Vanguard ta yi dashi inda yace Tinubu ya san ‘yan siyasa kuma yasan me suke da bukata kuma yana musu.

Yace amma ya kasa mayar da hankali dan fahimtar abinda mutane ke bukata dan su ma ya musu.

Yace Mutane abinda suke bukata shine tsaro da kawar da talauci.

Yace abinda ya kamata Tinubu ya fahimta shine ba sai ya tara ‘yan siyasa a jikinsa ba, idan ya biyawa Talakawa bukatunsu zai iya cin zabe.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sabuwar Wakar Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da matar Rarara, Aishatulhumaira ta yi ta jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ta yaya ta yi waka da wanda ba mijinta ba?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *