
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kashe naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da ke jihar Neja a tsakiyar ƙasar, wadda ambaliya ta lalata.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a yau Asabar, yayin da shi kuma Ministan Ayyuka David Umahi ya ce shugaban ya amince da yin irin wannan aiki a jihohi da dama.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da minista [na ayyuka]. Tattaunawa kawai muka yi da shi kafin mu je wajen shugaban ƙasa, wanda shi kuma ya amince. Abu ne mai muhimmanci ga al’umma,” a cewar Idris.
Umahi ya ce sauran jihohin da za a yi aikin sun ƙunshi gadar Wukari a jihar Taraba, da gadar Lokoja a jihar Kogi, da gadar Afikpo a jihar Ebonyi, da gadar sama ta Keffi a jihar Nasarawa, da gadar Jebba a Kwara, da gadoji bakwai a jihar Edo, da kuma wata gada a jihar Kebbi.