Wednesday, May 7
Shadow

Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman kiristoci, Bishop Matthew Hassan Kukah da Pastor Tunde Bakare suka soki Gwamnatinsa.

A sakonsu na bikin Easter, Manyan malaman kiristocin sun nemi shugaban kasar ya dauki matakai akan matsin tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama da ita.

Saidai da yake mayar da martani ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala, shugaba Tinubu yace a wasu bangare da Fasto Tunde Bakare ya sokeshi sun sha banban amma kuma yana da ‘yanci a matsayinsa na dan kasa ya bayyana ra’ayinsa.

Yace amma shugaban kasar ya mayar da hankali wajan ganin ya cika alkawuran da ya daukarwa ‘yan Najeriya.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar shugaba Tinubu yayiwa majalisar zartarwa garambawul

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *