Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Plateau da Benue da kuma Kwara.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Najeriya.
A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ƴan Najeriya da basu ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar.
Shugaban ƙasan wanda ya shafe fiye da sa’oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar.
Sanawar ta ayyano shugaba Tinubu yana shaidawa hafsashin tsaron cewa daga ɓangarensa fa tura ta riga ta kai bango, domin haka wajibi ne su tashi tsaye domin samar da mafita game da halin da Najeriya ke ciki a kan tsaro.
Dama dai shugaban ƙasar ya umarci shugabannin tsaron su yi aiki tare da hukumomin jihohin da ke da matsalolin tsaro a Najeriya domin cimma matsaya a kan matakin bai ɗaya da ya fi dacewa a ɗauka a kai tun daga tsuhe.