
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma, Leo XIV da za a gudanar a birnin Rome na asar Italiya.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Tinubu zai tafi Rome a ranar Asabar domin halartar bikin, bisa gayyatar da sabon fafarman ya aike masa.
Sanarwar ta ce Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariar Katolika na Najeriya domin shaida bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267.
Fadar shugaban ƙasar ta ce cikin takardar gayyatar sabon fafaroman ya bayyana alaƙar ƙashin kai da Najeriya, yana mai cewa ”ƙasarka mai girma na da mutuƙar muhimmanci a gareni, saboda na yi aiki a majami’ar Apostolic Nunciature da ke birnin Lagos a shekarun 1980”.