
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai yi takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 ba, sannan zai mara wa Tinubu baya.
Wike ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da sashen Pidgin na BBC, inda ya ce har yanzu shi ɗan jam’iyyar PDP ne.
“Ba zan sake yin takara ba. Ba zan yi takara da mutumin da nake yi wa aiki ba. Waye zai yi nasara idan ba shi ba?” kamar yadda Wike ya faɗa.
Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers, ya yi takarar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP don zama ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sai dai ya yi rashin nasara a hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
Ministan na Abuja ya kuma nuna ɓacin-ransa kan matakin jam’iyyar na kin ware tikitin takarar shugaban ƙasa wa yankin kudu, abin da ya janyo ta faɗa rikici da ya yi mata nakasu a zaɓen da ya gabata.
Wike ya kuma soki wasu jagororin jam’iyyar, sai dai ya ce babu inda zai je yana nan a PDP daram.