
Gwamnan jihar Wisconsin ta kasar Amirka, Tony Evers ya nemi a canja sunan uwa a daina kiranta da mahaifiya a rika kiranta da ma’ajiyar Maniyyi.
Ya bayyana hakane a cikin kasafin kudin da ya kai majalisar jiharsa inda ya kuma bukaci a canja sunan mahaifi da mata da miji duka.
Saidai da yawan ‘yan kasar Amurkar basu yi na’am da wannan shawara tasa ba inda suka rika sukarsa da cewa wannan cin zarafin mahaifiyane.