
Rahotanni sun bayyana cewa, dala Miliyan $3 ce aka ware aka rabawa sanatocin Najeriya dan su amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Rahoton yace a gidan Kakakin majalisar, Godswill Akpabio aka raba wadannan kudade a tsakannin ranekun Talata da Laraba.
Rahoton yace wasu daga cikin sanatocin sun samu dala dubu $10 inda wasu suka samu dala Dubu $5 ya danganta da girman mukamin sanata.
Rahoton ya kara da cewa Akpabio ya kira wasu sanatoci musulmai zuwa gidansa shan ruwa inda anan ne ya basu kasonsu, saidai wasu sanatoci ciki hadda tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal basu amsa wannan gayyata ba.
Rahoton yace Wike ne ya baiwa Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio kudaden da aka raba.