Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya naɗa Elon Musk a matsayin shugaban sabuwar ma’aikatar inganta ayyukan gwamnati.
Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare da Musk a ma’aikatar ta Department of Government Efficiency (Doge).
Sunanta ya yi kama da sunan kuɗin kirifto da Elon Musk ya fi so mai suna Dogecoin, kuma an ƙirƙire ta ne domin kawo ƙarshen wahalhalu a harkokin gwamnati.
Mutanen biyu za su dinga bai wa fadar White House ƙarƙashin gwamnatin Trump shawara ne kan “yadda za a gudanar da manyan sauye-sauye,” a cewar Trump.
Tun da farko, Trump ya sanar da naɗa mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta Fox, Pete Hegseth, domin ya zama sakataren tsaro, sannan ya John Ratcliffe shugaban hukumar leƙen asiri ta CIA.
An daɗe ana sa ran Musk, wanda ya fi kowa kuɗi a duniya, zai shiga gwamnatin ta Trump bayan ya bai wa kwamatin yaƙin neman zaɓensa maƙudan kuɗaɗe.
Ramaswamy ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Republican kafin daga baya ya janye kuma ya mara wa Trump baya.