Sunday, January 26
Shadow

Tsaffin Janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya>>Oshiomhole

Tsohon Gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa, tsaffin janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya.

Oshiomhole ya bayyana hakane a yayin da shugaban kwamitin dake kula da harkar hakar ma’adanai a majalisar,Sampson Ekong ke muka sakamakon binciken kwamitinsa ga majalisar.

Oshiomhole wanda shine shugaban kwamitin dake kula da harkokin cikin gida ya bayyana cewa, sun san wadannan tsaffin janarorin dan kuwa koda a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sai da ya rubuta mai wasika akan ayyukan nasu.

Ya kara da cewa, wadannan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba suna safarar muhgan makamai dan gudanar da ayyukansu kamar yanda ake yi a sudan ta kudu.

Karanta Wannan  Shin matakan tsuke bakin aljihun CBN na tasiri wajen rage hauhawar farashin kaya a Najeriya?

Oshiomhole ya bayar da shawarar cewa, maganin wannan matsala shine a samar da rundunar jami’an tsaro da zata yaki wadannan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *