Friday, December 5
Shadow

Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam’iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP

Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam’iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP

Tsohon Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar yaƙi ya karɓi katin zama ɗan Jam’iyyar ADC, a yayinda ake ci gaba da jita-jitar cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai yi takara a shekarar 2027.

Atiku, wanda a ƴan kwanakin baya ya fita daga jam’iyyar PDP bayan ɗaukar tsawon lokaci ana rigingimu, an tsara zai karɓar katin jam’iyyar ADC.

Atiku dai zai karɓi katin jam’iyyar ADC a garin sa na Jada da ke ƙaramar hukumar Jada ta Adamawa, an tsara cewa zai karɓi katin jam’iyyar a ranar Laraba 6 ga watan Agusta, amma aka ɗage karɓar katin ba tare da wani bayani ba.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta Karbi Harajin Naira Biliyan 625.13 daga hannun 'yan Najeriya daga watan Janairu zuwa Satumba na 2025

Daga Usman Salisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *