
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo ya cika shekaru 88 a Duniya.

An haifeshine a rana irin ta yau, 5 ga watan Maris na shekarar 1937.

Kuma ya taba zama shugaban soja na Najeriya daga shekarar 1976 zuwa shekarar 1979.
Kuma ya sake zama shugaban kasa na mulkin farar hula daga shekarar 1999 zuwa 2007.