
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce mutane da dama a Najeriya sun daina yarda da bangaren shari’a wajen samun adalci.
Mista El-Rufai ya kuma zargi bangaren shari’ar da cin hanci da rashawa, yana cewa wasu alkalai da lauyoyi sun sauka daga abinda ke kansu ta hanyar karkata ko karɓar rashawa wajen yanke hukunci.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin makon shari’a na kungiyar lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Bar Association), reshen Bwari, da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa rashin amincewar jama’a ga shari’a na da nasaba da yawan jinkiri wajen yanke hukunci da kuma shawarwarin da ake ganin sun samo asali daga son rai ko tasirin wasu masu hannu da shuni a waje.
“A gefe guda, bangaren shari’armu—wanda ya kamata ya zama ginshikin adalci —yana fuskantar bincike mai tsanani. Damuwar da ake da ita kan jinkirin shari’a, matsalolin tsarin shari’a, da a wasu lokuta, alkalan da ke karkata (idan za a fadi hakan a hankali), duk suna rage kwarin gwiwar jama’a,” in ji shi.