
Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya je Kaduna a karshen mako kuma yaga yanda Gwamnatin jihar ke ta ayyukan raya kasa.
Yace irin abinda suke nema a Kano kenan tun shekara 1999.
Saidai ‘yan Kaduna da yawa sun yi caaa a kansa inda suke tambayar shi cewa wace Kadunar ya je?