Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce wahalhalu da “sadaukarwar” da ‘yan ƙasar suka yi ba su tashi a banza ba tun bayan hawa mulkinsa a watan Mayun 2023.
Da yake bayani cikin saƙonsa na sabuwar shekara da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce sabuwar shekarar “za ta kusanta mu da kakkyawar Najeriya da muke ta hanƙoro”.
A cewarsa: “Gare ku ‘yan ƙasa, sadaukarwar da kuka yi cikin wata 19 da suka wuce ba ta tashi a banza ba. Ina tabbatar muku cewa kuma ba za ta tashi a banza ba nan gaba. Mu ci gaba da aikin gina ƙasa tare.”
Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ƙara mayar da hankali wajen aiwatarwa da kuma “bijiro da sauye-sauyen da suka zama wajibi” domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya