
Kakakin Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa sharri ake masa rahoton dake cewa wai ya zagi shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Rahotan wanda wata kafa me suna Rant HQ Politics ta wallafa tace Akpabio yace ai a Najeriya ake Shekye mutane ba’a Amurka ba dan haka Ba ruwan Trump da Najeriya.
Saidai a sanarwar daya fitar, Akpabio yace shi bai fadi wannan magana ba, sharri aka kala masa.
Akpabio yace yana girmama Trump a matsayin shugaban kasa me karfi sannan ba zai tsoma bakinsa akan abinda ke faruwa a kasar Amurka ba.