Friday, December 5
Shadow

Wani asibiti ya yi ragin kashi 50 na kuɗaɗen aiyuka a Kano

Wani asibiti ya yi ragin kashi 50 na kuɗaɗen aiyuka a Kano.

Wani asibitin mai suna Best Choice ya yi ragin kaso 50 na kuɗaɗen ayyukansu na yau da kullum, wanda suka haɗa da kudin ganin likita kudin Gado da sauran ayyukan su, shi kuma bude Fayal ya zama kyauta ne yanzu haka.

Hakan na kunshe ne Cikin wata tattaunawa da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal yayi da Jaridar Alfijir Labarai a yau Talata.

Lawal yace bayan korafe-korafe da kiraye-kirayen da jama a suke ta yiwa asibitin hukumar gudanarwar sun yi kwakkwaran bincike har suka gano yadda wasu suke kasa zama har lokacin da ya dace likita ya sallamesu yayi suke tafiya, sannan wasu kuma tun daga bude fayil suke kasawa duk da yadda suke kaunar zuwa asibitin, wannan dalilin ne yasa suka ɗauki wannan matakin domin farantawa al’umma duk da irin kuɗaɗen da suke kashewa ga tsadar komai ga kuma yadda ake bawa asibitin cikakkiyar kulawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ta dauki hankula saboda rawar Bhadala sanye da Hijabi

A baya muna buɗe fayil na mutum daya akan dubu 20, shi kuma na iyali dubu 40 yanzu haka ya koma kyauta.

Shi kuma ganin likita dubu 10 ne, amma yanzu ya koma dubu 5. Kudin gado dubu 70 ne, amma yanzu mun mai dashi dubu 35 babban dakin, akwai na dubu 50, ya koma dubu 25, dakin dubu 25, ya koma dubu 12,500, sai ɓangaren masu awo shine daga dubu 150,000 ya koma dubu 80, haihuwa itama daga dubu 150,000 ta koma dubu 80, sai CS daga dubu dari 6, ya dawo dubu dari 3, haka sauran gwaje-gwajen ma duk suma haka zasu koma domin a kara kyautatawa al’umma, Allah ya kare mu da lafiya baki daya ameen.

Karanta Wannan  Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta gurfanar da tsohon dan majalisa a kotu bisa zargin satar Naira Miliyan 18 inda kotu ta bayar da belinsa akan Naira miliyan 20

A karshe a madadina da iyalaina da maaikatana Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Marigayi Alh Aminu Dantata da gwamnatin Kano da al’ummar Kano da Afrika baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *