Sunday, March 16
Shadow

Wani bawan Allah ya rasu ana tsaka da Sallar Asuba

Wani bawan Allah me suna Salihu Byezhe ya rasu ana tsaka da sallar Asuba tare dashi.

Lamarin ya farune a kauyen Gudaba dake Kuje a babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin garin me suna Musa Dantani yace Salihu ya rasu ne a yayin da yake Sallar Asuba a masallacin garin.

Yace Salihu ya gama yin Sahur ya tafi masallaci, ana tsaka da sallah ya yanke jiki ya fadi, an garzaya dashi Asibitin Kuje inda acan Likita ya tabbatar da ya rasu.

An alakanta rasuwar tashi da hawan jini.

An yi jana’izarsa da misalin karfe 10:12 am kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Karanta Wannan  Namijin Duniya: Wani matashi daga jihar Naija ya auri mata 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *