Friday, December 5
Shadow

Wani tsohon Gwamna ne daga kudancin Najeriya ake zargi da daukar Nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin Mhulki, Ana shirin fara bincikensa

Rahotanni sun bayyana cewa, Wani tsohon Gwamnane daga kudancin Najeriya ake zargi da hannu a shiryawa yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.

Rahotanni sun ce ana zargin Tsohon Gwamnan ne ya samar da kudaden da za’a gudanar da juyin mulkin kamar yanda gidan jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton yace har yanzu ana binciken alakar dakar tsakanin tsohon Gwamnan da sojojin da suka shirya juyin mulkin, kuma da zarar an samu tabbacin hannunsa, za’a gayyaceshi dan amsa tambayoyi.

Rahoton yace ana kiyaye sunayen sojojin da suka shirya juyin mulkin dan kada a fitar dasu amma Daily Trust tace ta samu cewa akwai soja Brigadier general da kuma Captain.

Karanta Wannan  An baiwa Tinubu Shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa

Tace kuma ana sojojin daya ya fito daga jihar Naija ne yayin da dayan ya fito daga jihar Nasarawa kuma yana da alaka da gidan Sarauta sannan kuma dan uwane wajan tsohon gwamnan jihar Nasarawar, Tanko Almakura.

Daily tace iyalan sojan, Musamman matarsa tana cikin damuwa sosai inda take fatan Allah yasa kada a sameshi da laifin da ake zarginsa dashi.

Itama dai jaridar ta Daily Trust tace ta samu rahoton dake tabbatar da cewa, lallai an shirya yiwa shugaba Tinubu juyin mulki, duk da Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *