
Wani magidanci a Legas dake unguwar Victoria Garden City ya hallakà yaron aikin gidansa bayan kamashi yana aikata Alfasha da matarsa.
Yaron aikin dan kimanin shekaru 20 sunansa Nengak kuma dan asalin jihar Filato ne wanda aka daukeshi aiki a gidan yana kai yara makaranta da aiken cefane da sauransu.
Me gidan ya fara jin rade-radin cewa yaron na lalata da matarsa.
Dalilin haka ya saka kyamarar CCTV kuma ya kamasu turmi da tabarya.
Anan ya gayyato yaran layi sukawa yaron aikin gidan nasa duka har ya mutu.
Abokin mamacin Bitrus Idi ne ya bayyana haka ga kafar Daily Post inda yace gawar sa na mutuware an ki basu inda ‘yansanda suka ce sai sun biya kudi an yi bincike kan dalilin mutuwar tasa.