
Wani barawon dota me suna Akeem Jimoh dan kimanin shekaru 28 ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari.
Doyar da ya sata dai darajarta Naira dubu talatin da biyarne watau 35,000.
Barawon dai ya amsa laifinsa bayan da aka gurfanar dashi a gaban kotu dake Osogbo jihar Osun.
Yayi satar ne ranar Juma’a da misalin karfe 10 a watan July 25, 2025 kuma doyar da ya sata sanda 17 ce.
Barawon dai bashi da lauya, kuma da aka tambayeshi dalilin yin wannan sata, yace yunwa ce ta sakashi hakan inda ya roki kotu ta tausaya masa.
Sunan wanda akawa satar, Tiamiyu Abegunde.
Rahoton yace me gabatar da kara Babatunde Olukokun yace Akeem Jimoh yace an taba yi mai daurin shekaru 3 a gidan yari bayan da ya tsayawa wani ya karbi belinsa amma wancan din ya tsere.
Mai shari’a, Magistrate, Muibah Olatunji ta aika Akeem Jimoh gidan yari tsawon shekaru 3 tare da aikin wahala sosai kuma ba tare da bashi zabin biyan tara ba.