Sunday, March 16
Shadow

Wasu Kiristoci Musamman daga kudancin Najeriya na yiwa Jihohin da suka bayar da hutun Ramadan Dariya

Wasu Kiristoci Musamman daga kudancin Najeriya na yiwa jihohin musulmai da suka bayar da hutun watan Ramadana Dariya.

A ganinsu, wannan hutu koma bayane ga ci gaban kasa.

Bayan wallafa labaran da kafafen watsa labaran Najeriya suka yi, an samu wasu na bayyana ra’ayoyi kamar haka:

Wani me suna King Premier ya bayyana cewa suna Bankuna ya kamata a rufesu, ba makarantu kadai ba.

Shima wani me suna AlleZamani ya tambaya cewa shin zuwan Ramadan yasa an kulle makarantu a kasar Saudi Arabia? Inda ya kara da cewa ina zaune da sakarkarun mutane a kasa daya.

Binciken da Shafin Hutudole yayi ya gano cewa, a kasar Saudiyya ba’a kulle makarantu ba amma an rage lokutan karatune saboda zuwan watan Ramadan.

Karanta Wannan  Kalli Yanda wasu 'yan Najeriya suka yi bikin murnar cin zaben shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Wani me sunan Nigeria Exchange rate yace nan gaba kuma irin wadannan jihohi sai su rika neman masu zuba jari. Yace su tabbatar sun baiwa masu zuba jarin sharadin cewa dole su zama musulmai, wanda basu da aure ko basu da yara.

Jihohin Kano, Katsina, Kebbi da Bauchi ne suka bayar da hutu saboda zuwan Asumin watan ramadana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *