
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, wata budurwa ta kashe kanta.
Lamarin ya farune a rukunin gidaje na CITEC dake Life Camp, babban Birnin Tarayya, Abuja ranar April 22, 2025.
An iske matar da misalin karfe 7:00 a.m. rataye a jikin wata kwantena inda ‘yansanda suka isa wajen suka tafi da ita zuwa FMC Jabi inda a canne likitoci suka tabbatar da ta mutu.
An dai gano wayarta sannan an fara bincike kan lamarin.