Mutane sama da dubu biyar ne aka kwantar a Asibiti a kasar Ingila biyo bayan bullar wata cutar mura.
Mutanen sun kamu da cutar ne a makon karshe na shekarar 2025 inda gadaje suka yi kadan a Asibiti sai da aka samar sa sabbin gadaje na gaggawa 1,300.
An dai bayyana sunan cutar da norovirus and Respiratory Syncytial Virus (RSV) kuma yawan masu kamuwa da ita din sun fara karuwane daga ranar Kirsimeti.
Daraktan hukumar kula da lafiya ta kasar, Julian Redhead ya bayyana cewa, abin damuwa ne ganin cewa mutane 5000 ake kwantara kullun a Asibiti sanadiyyar cutar.
Yace kuma nan gaba lamarin zai kara munana saboda ana tsammanin sanyi ya karu.
Yayi kira ga mutane su dauki matakan baiwa kansu kariya.