
Rahotanni sun ce ana tsammanin jam’iyyar APC zata dauki nauyin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben shekarar 2023 Dumebi Kachikwu ya kai su Atiku kara kotu.
Dumebi Kachikwu ya bayyana cewa au Atiku sun je jam’iyyar ADC ne dan su musu kwace.
Inda yace bai yadda da hakan ba zai garzaya kotu dan kai su kara.
Farfesa a bangaren kimiyyar siyasa daga jami’ar Jihar Nasarawa, Jideofor Adibe yace akwai yiyuwar APC zata dauki nauyin Kachikwu ya kai su Atiku kara.
Ya bayyana cewa wannan dama ce ga dan takarar ya samu suna sosai a Duniya.
A zaben shekarar 2023, Kachikwu na 5 yazo.