
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankin Fidelity Bank na fuskantar barazanar durkushewa.
Hakan ya bayyana ce bayan da Kotun Koli ta bukaci bankin ya biya wani bashi na Naira Biliyan N225 da ake binsa.
Bankin dai idan har zai biya wadannan kudade rahoton yace durkushewa zai yi.
Saidai wasu masana harkar bankin sun ce basa tunanin babban bankin Najeriya, CBN ,zai bari bankin ya durkushe, zai iya kai masa dauki.