
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar EFCC na shirin kama shugaban jam’iyyar ADC, David Marka da kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.
Jam’iyyar ADC ce ta bayyana hakan ta bakin kakakinta, Bolaji Abdullahi.
Jam’iyyar tace me yasa sai ‘yan ADC ne kadai ake wa irin wannan bincike kuma me yasa Misali David Marka da ya bar shugabancin majalisar dattijai kusan shekaru 10 da suka gabata, sai yanzu ne za’a fara bincikensa?
ADC ta zargi EFCC da kawar da kai akan ‘yan jam’iyyar APC bata bincikensu.
Hakan na zuwane bayan sakin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC din ta yi bayan kamashi.