
Dan Jarida dan asalin Najeriya dake zaune a kasar Amurka, Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa, kamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Ya saki matarsa, A’isha.
Farooq Kperogi ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook ranar Laraba.
Ya bayyana hakane a martani ga labaran dake yawo cewa A’isha tace Buhari kamin ya rasu ya ce mata ta nemar mai gafarar ‘yan Najeriya.
Farooq Kperogi yace bai san ingancin wannan labari ba amma abinda ya sani shine A’isha Buhari basa tare sa mijinta kamin ya rasu ya saketa.