Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa: Kasar Amurka ta ce bata amince da tsayar da Kìsàn Falasdiynawa ba a Gàzà

Amurka ta hau kujerar na-ƙi game ƙudirin da aka gabatar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a yaƙin Gaza ta dindindin ba tare da sharaɗi ba.

Sauran mambobin kwamitin 14 sun amince da buƙatar ƙudirin, wanda kuma ya buƙaci sakin duka Isra’ilawa da ake garkuwa da su tare da ɗage taƙaita shigar da agaji zuwa Gaza.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniyar, Dorothy Camille Shea, ta ce ƙudirin ya gaza shafar kowane ɓangare saboda bai yi kira ga Hamas ta ajiye makamanta tare da ficewa daga Zirin Gaza ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Yanda Yusuf Buhari, da Shugaba Tinubu da Seyi Tinubu sa sauransu sukawa Gawar shugaba Rakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *