
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar ADC.
Ya kuma bayyana cewa, Peter Obi yake son ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa sai Kwankwaso ya masa mataimaki.
An dauki wannan matakinne dan a kayar da Atiku kada ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC.
Hakanan Rahoton wanda Jaridar Daily Trust ta ruwaito yace tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida me ritaya shima ya gayawa Kwankwaso ya koma ADC.
Hakan na zuwane yayin da ake ganin Atiku ne zai lashe tikitin takarar shugaban kasa a ADC idan Kwankwaso da Peter Obi basu hada kai ba.